Tsohon Kwamishina kuma mamba a Kwamitin Gudanarwa na Hukumar Hajji ta Ƙasa, NAHCON, Dafta Adam Idoko ya rasu.
Ya rasu a asibiti a Abuja bayan ya sha fama da jiyya.
Marigayi Idoko, wanda ya fito daga yankin ƙabilar ibo, mahaifi ne ga Barista Fauziyya ta sashin shari’a na NAHCON.
Tuni dai a ka binne marigayin a maƙabartar Gudu da ke Abuja, a bisa koyarwar addinin Musulunci.
Ƙarin bayani na nan tafe…




