A ƙalla mutane uku ne aka rawaito cewa sun rasu bayan da motar bos mai ɗauke da alhazan Ummara 16 ƴan Ƙasar Egypt ta yi karo da raƙumi a Saudi Arebiya, in ji Ma’aikatar Harkokin Waje ta Egypt ɗin.
Hatsarin ya faru ne a wajen kilomita 310 daga garin Tabuka, wanda yake a arewa maso yammacin Saudiya yayin da Alhazan ke kan hanyar su ta zuwa Makka domin yin Ummara, inji Mataimakin Ministan Ƴan ƙasar Egypt da ke zama a kasashen waje a wata sanarwa da ya fitar.
“Ofishin Jakadancin Egypt na Jidda ya bibiyi lamarin matuƙa kuma yana tuntuɓar mahukunta a Saudiyya domin shirye-shiryen dawo da zuwa ƙasar su da kuma bincika sanadiyyar hatsarin,” in jishi.
Mutane 3 ne dai suka rasu ana kawo su asibiti, inda mutane 13 suka samu raunuka daban-daban kuma suna karɓar magani.





