HAJJIN 2025: Kano ta tsayar da ranar rufe ƙarbar kuɗaɗen ajiya na maniyyata

0
246

Hukumar jin dadin alhazai ta jihar Kano ta sanar da ranar 1 ga watan Junairu 2025 a matsayin ranar rufe karbar kudaden ajiyar maniyyata Hajjin 2025.

Wannan sanarwar ta fito ne daga bakin babban daraktan hukumar Alhaji Lamin Rabi’u Danbappa yayin wani taron hadin gwiwa da ma’aikatan hukumar da jami’an cibiyar alhazai na kananan hukumomi da aka gudanar yau a ofishin sa.

Alhaji Lamin Rabi’u Danbappa ya jaddada cewa wa’adin ya yi daidai da kalandar aikin Hajji na 2025 da Hukumar Alhazai ta Najeriya (NAHCON) ta fitar, wanda ya wajabta wa dukkan jihohin kasar da su mika bayanan maniyyatansu ga Hukumar ko kuma kafin ranar 1 ga watan Janairun 2025.

Daga nan sai ya jaddada muhimmancin bin wannan umarni domin tabbatar da kammala duk abinda ya kamata ayi cikin sauki da natsuwa.

Bayan haka sai ya hori kananan hukumomin da su mike tsaye wajen wayar da kan mutane ganin sun kammala biyan kuɗaɗen ajiyan su kafin ranar sa aka kebe don rufe karɓa.

Sannan kuma ya hori shugabannin hukumomin na kananan hukumomi su kirkiro sa dabarun yadda za su talkata wa mutane kujerun Hajjin a kananan hukumomin su