Babban Bankin Najeriya CBN zai samu N5.4bn daga kudin aikin Hajjin 2026

0
125
CBN zai samu N5bn daga aikin Hajjin 2026. Hoto daga HAMS/AFP/Getty Images)

Ana hasashen Babban Bankin Najeriya (CBN) zai samu kusan Naira biliyan 5.4 a matsayin kudin gudanar da hada-hadar kudade daga aikin Hajjin shekarar 2026.

Wadannan alkaluma sun ci karo da ikirarin gwamnati na cewa ba ta samun wani kaso ko riba daga aikin Hajji a Najeriya.

Wani nazari da aka yi kan kudin aikin Hajji na 2026 ya nuna cewa kowane mahajjacin Najeriya zai biya kashi biyu cikin 100 na kudin da aka amince da shi a matsayin kudin sabis da CBN ke yi.

Yayin da aka kayyade kudin aikin Hajji a kan Naira miliyan 7.6, kowane mahajjaci zai biya biyan kusan Naira 136,417 a matsayin kudin sabis din kenan.

Bisa kididdigar da aka yi kiyasin mahajjata 40,000 da ake sa ran za su halarci aikin Hajjin shekarar 2026, adadin kudin da CBN zai samu ya kai kimanin Naira biliyan 5.3.

A farashin dalar Amurka kuwa, za a caji ko wane mahajjaci dala 92.46, wanda hakan ya kai kusan dala miliyan 3.7.

Idan dai za a iya tunawa, a watan Oktoban shekarar da ta gabata, ‘yan jaridu masu aikin rahoto kan Hajji sun roki gwamnatin tarayya da ta daina biyan kudin sabis din na kashi biyu cikin dari, tare da bayyana hakan a matsayin abin da bai kamata ba.

Sai dai duk da wannan roko, babu wata sanarwa a hukumance na janye wannan mataki daga CBN ko gwamnatin tarayya.

Sai dai wata majiya mai tushe ta shaida wa Hajj Reporters cewa ana ci gaba da tattaunawa da kiraye-kirayen kan lamarin.