Shin kun san cewa akwai hanyoyin gudanar da aikin Hajji iri uku? Ga bambancinsu

0
112
Hajjin bana: Maniyyaciya daga Najeriya ta maida dalar Amurka 5,000 da ta tsinta ga wani maniyyaci ɗan ƙasar Russia

Shin kun san cewa akawai yanayin aikin Hajji daban-daban?

Duk lokacin da mahajjaci zai gudanar da ibadarsa, akwai salo kala uku da zai iya yin aikin Hajjinsa: wato Ifrad, Tamatu da kuma Qiran.

Hanyoyin nan guda 3 suna ba wa mahajjata damar zaɓen salon da zai ba su damar yin ‘Umrah ko Hajji cikin sauƙi.

A wannan makala an yi bayanin bambance-bambance tsakaninsu.

Sai dai kafin mu yi bayanin bambance-bambancensu akwai bukatar mu yi karin bayani mene ne su da alakarsu da aikin Hajji da Umrah.

  1. Mene Hajji da Umarah?

Hajji da Umrah ibadu ne a cikin Musulunci. Hajji shi ne farilla ga wanda yake da iko, Umarah kuma Sunnah ce.

Hajji da ‘Umrah duka sun kunshi tafiya zuwa Makkah wadanda suka shafi wasu ayyuka kamar ihrami, dawafi a Ka’aba, yin Safa da Marwah, da aske gashi.

  1. Mene ne bambancin Hajji da Umarah?

Wani abin da ya bambanta Hajji da Umarah shi ne cewa akwai takamaiman lokacin ake aikin Hajji yayin da ita kuma Umra ana iya yin ‘Umrah a kowane lokaci a cikin shekara.

Bugu da kari, hajji da umrah sun bambanta dangane da hukuncin kowannensu, kamar yadda bayani ya gabata.

Bari mu duba hanyoyi da muka bayyana tun a farko don fahimtar nau’ikan Hajji guda uku:

Ifrad (Hajji kadai)

Alal misali, Ali yana zaune a kasar Saudiyya kuma ya riga ya yi Umrah sau da dama a shekarun baya. Saboda yana zama a can don haka ya saba yin umrah kowane lokaci.

Mu kaddara a ranar 8 ga Zul-Hijjah – kwana daya kacal kafin ranar Arafah, sai ya ga mahajjata sun burge shi kawai sai ya ji sha’awar yin aikin Hajji. Ya shirya kayansa da sauri ya nufi Makkah.

Sai dai Ali ba shi da isasshen lokacin da zai yi Umra da aikin Hajji, saboda haka ya yanke shawarar yin Hajji kawai. To saboda ya taba yin Umrah da dama kuma zai iya yin wasu Umrah a nan gaba, sai ya gudanar da aikin Hajji kadai a wannan yanayi.

Wannan shi ake kira da Ifrad, yadda mahajjaci zai gudanar da aikin Hajji ba tare da ya yi Umrah ba

Qiran (Hajji da Umrah a tare)

A nan kuma alal misali, mutum dan kasuwa ne wanda a kowane lokaci yana aiki ko kasuwa, saboda haka ba shi da isasshen lokacin da zai tafi wani wuri sama da mako guda.

Sai mutum ya yi niyyar yana son ya yi aikin Hajji da Umrah amma babu isasshen lokaci, watakila kwana 5 kawai yake da shi; to a nan zai sai ya tafi Makkah a ranar 8 ga watan Zul Hijja kuma ya dawo 12 ga watan na Zul Hijja.

Sabida haka ba zai iya yin aikin Hajji da Umrah a wadannan kwanakin ba.

Abin da ya fi a nan shi ne mutum ya yi salon Hajji da ake kira da Qiran.

Yadda zai yi shi ne, mutum zai yi niyyar yin aikin Hajji da Umrah a tare, amma kuma zai gudanar da ibadar da ake yi ta aikin Hajji ne kawai amma kuma da niyyar Hajji da Umrah. Kuma ibadarsa ta karbu.

Tamatu (Umrah daga baya a yi aikin Hajj)

A wannan salon, mutum ne watakila yana so ya yi aikin Hajji a wannan shekara, amma kuma bayan dogon lokaci yana tara kudade, yanzu Allah ya yi.

Sai kuma ya isa Makkah watakila sati biyu kafin a fara aikin Hajji.

Mutum zai iya fara yin Umrah kafin lokacin, saboda watakila wannan ce dama daya da mutum yake da ita.

Saboda haka a wannan yanayin mutum zai iya fara yin Umrah, sai ya cigaba da zamansa kafin zuwan lokacin aikin Hajji.

Wadannan salo guda uku suna nuna yadda bambance-bambancen hanyoyin Hajji.

Wato;

  • Idan mahajjaci ya yi aikin Hajji kawai, shi ake kira Ifrad.
  • Idan mahajjaci ya yi aikin Hajji kawai amma da niyya biyu shi ake kira Qiran. A nan ana yin niyyar Hajji da Umrah ne amma kuma Hajji kawai za a yi.
  • Idan mahajjaci ya yi’umrah, sannan ya huta kafin zuwan lokacin aikin hajji shi ake kira da Tamatu’.

DAGA HAJJ REPORTERS: