An yi kira ga hukumar alhazai ta Najeriya NAHCON da ta duba yiwuwar kara wa’adin biyan kudin aikin Hajjin bana na shekarar 2026.
Wani mai sharhi kan lamuran yau da kullum, Suleiman Salihu Mu’azu, ne ya yi wannan kiran inda ya ce akwai bukatar a tsawaita wa’adin da aka tsara zai dakata daga 28 ga watan Janairu.
A cikin wata wasika, wacce ya aika wa hukumar NAHCON da sauran hukumomin jin dadin alhazai na jihohi, Mu’azu ya ce matakin ya kamata duba yanayin tattalin arziki da kalubalen da ke fuskantar mahajjata da hukumomin a jihohi.
Ya kara da cewa hauhawar farashin kaya da kuma canjin kudaden waje a baya-bayan nan sun sa an samu koma baya da raguwar masu zuwa aikin hajji da dama, musamman manoma da ‘yan kasuwa, wanda hakan ya sa zai yi musu wahala su iya kammala biyan kafin wa’adin.
A cewarsa, tsawaita wa’adin zai kuma taimaka sosai wajen samun shigar masu ruwa da tsaki da kuma kungiyoyin da suka kamata tare da daidaita shirye-shiryen sufuri.
Mu’azu ya bukaci hukumar da ta yi la’akari da shawarar domin a samu gudanar da aikin Hajji cikin kwanciyar hankali da kuma hada kan al’umma, inda ya kara da cewa tsawaita lokacin zai rage matsin tattalin arziki da ake fuskanta ga mahajjata ba tare da kawo cikas ga shirye-shiryen da ake da su ba.





