Kiran da Independent Hajj Reporters (IHR) ta yi wa gwamnonin jihohi kwanan nan na su samar da kuɗaɗe kafin Hajjin 2026, hakan ya ja hankulan masu ruwa da tsaki a ɓangaren aikin Hajji. Duk da cewa wasu na ganin wannan buƙata ba ta da amfani, amma yana da muhimmanci a bayyana dalilan da ke tattare da wannan kira da kuma dalilin da ya sa tallafin kuɗi na wucin-gadi ya zama wajibi.
Dokar da ke jagorantar shirye-shirye gabanin tafiya Hajji ta samo asali ne daga hukumomin Saudiyya, kuma tana aiki a kan ƙasashe 162 da ke halartar Hajji. Sai dai tsarin rajistar maniyyata a Najeriya yana ɗaukar lokaci mai tsawo, wanda hakan ke jinkirta aika kuɗaɗe ga kamfanonin yi wa alhazai hidima na Saudiyya. Wannan jinkiri na haifar da matsala wajen cika sharuɗɗan biyan kuɗi da kwangila kafin lokacin Hajji.
A zahiri, tsarin adashin gata, wato Hajj Savings Scheme (HSS), ka iya zama hanya mafi sauƙi wajen tallafa wa maniyyatan da ke ƙarƙashin tsarin biyan kuɗi kaɗan-kaɗan, wato tsarin “pay-as-you-go”, biyan kuɗaɗensu. Sai dai har yanzu wannan tsari bai samu cikakken karɓuwa ba a tsakanin hukumomin hajji na jihohi.
Wata hanyar kuma ita ce, Hukumar Hajji ta Ƙasa (NAHCON) ta ɓullo da tsarin rajistar Hajji na shekara uku, wanda zai bai wa maniyyata damar biyan kaso 50 cikin 100 na farashin Hajji na yanzu don aikin Hajji na gaba. Wannan tsari na dogon lokaci zai taimaka wajen samun kuɗaɗe da wuri don shirye-shiryen Hajji.
Haka kuma, yana da muhimmanci a fahimta cewa, duk wani kuɗin da gwamnatocin jihohi suka bayar za a mayar da shi gaba ɗaya. Misali, irin wannan tsari ya samu nasara a jihar Jigawa a shekarun baya. Idan gwamnatin jiha ta biya kuɗin maniyyata 5,500, sannan aka samu mutum 4,500 ne suka kammala rajista, kuɗin kujerun 1,000 da ba a yi amfani da su ba za su dawo ta hanyar tsarin rajistar NUSUK.
Bugu-da-ƙari, jihohi na iya umartar hukumomin Hajji su riƙa mayar da kuɗaɗe a kowane mako bisa ga adadin maniyyatan da suka yi rajista, don tabbatar da gaskiya da riƙon amana wajen sarrafa kuɗaɗe.
Saboda haka, kiran da Independent Hajj Reporters suka yi ba wai neman tallafi ba ne, illa dai kira mai ma’ana na samun tallafin kuɗi na wucin-gadi don taimaka wa jihohi su cika sharuɗɗan biyan kuɗaɗe a kan kari kamar yadda Saudiyya ta gindaya. Wannan shiri na da nufin kare muradun maniyyatan Najeriya da kuma tabbatar da matsayin Najeriya a matsayin ɗaya daga cikin ƙasashe biyar mafi girma a Hajji a duniya, sannan ta kan gaba a nahiyar Afrika.



