HAJJI 2026: Ku Yi Koyi da Gwamnan Jigawa – Kiran CSO Ga Gwamnonin Jihohi

0
66

 

Cibiyar Independent Hajj Reporters (IHR) mai bibiya tare da yaɗa rahotannin ayyukan Hajji da Umara, ta yi kira ga Gwamnonin Jihohi 36 na ƙsar nan da su samar da tallafin rance ga Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta jihohinsu domin taimaka musu wajen biyan kuɗin Hajjin 2026 a kan kari.

 

Ta yi wannan kira ne a cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Lahadi mai ɗauke da sa-hannun babban jami’in IHR na ƙasa, Ibrahim Muhammad, inda ta bayyana cewa wannan kiran “ceto Hajjin 2026” ya zama dole duba da ƙarancin lokaci.

 

Ta ƙara da cewa, “Kalandar Hajjin 2026 ta wajabta wa kowace ƙasa ta kammala rajistar Hajji kafin ƙarshen watan Disamba mai zuwa, tare da umarnin cewa ba za a bayar da ƙarin lokaci ko kaɗan ba.

 

“Idan ba wannan tallafin aka samu ba, bai zama lallai maniyyata daga Najeriya su iya biyan cikakken kuɗin Hajji kafin ƙarewar wa’adin ba,” in ji IHR.

 

Cibiyar CSO ta kuma bayyana cewa, ƙarancin lokaci zai hana Hukumar Hajji ta Ƙasa (NAHCON) da Hukumomin Jin Daɗin Alhazai na Jihohi su shirya yadda ya kamata kafin Hajji, sai dai idan an samu kuɗaɗe ta hanyar rance da za a biya bayan alhazai sun kammala biyan kuɗinsu.

 

A cewar sanarwar, Gwamna Umar Namadi na jihar Jigawa ya riga ya amince da bayar da Naira biliyan 3.4 ga hukumar alhazai ta jihar domin ta shirya yadda ya kamata don amfanin maniyyatan jihar.

 

Gwamnan ya bayar da irin wannan tallafi a shekarar 2025, wanda IHR ke ganin abin koyi ne.

 

“IHR ta lura cewa tsarin rajistar Hajji mai ɗaukar lokaci, wanda ke ba jihohi damar yin rajista sannan su tura kuɗi zuwa NAHCON kafin a tura su zuwa ga kamfanonin yi wa alhazai hidima a Saudiyya, bai dace da tsarin wanda ya riga zuwa shi zai fara samun dama da Ma’aikatar Hajji da Umrah ta Saudiyya ke amfani da shi ba.”

 

Sanarwar ta ce, “Najeriya, a matsayin ƙasa ta biyar mai mafi yawan alhazai a duniya kuma mafi girma a Afirka, tana fuskantar ƙalubale wajen tsara kalandar aikin Hajji yadda ya kamata, wanda ke haifar da roƙon ƙarin lokaci wajen jigilar alhazai da sarrafa biza – wani yanayi mai ban kunya wanda za a iya kauce masa.”

 

“Saboda haka, muna roƙon Gwamnonin Jihohi da su ceci shirin Hajjin 2026 ta hanyar amsa wannan buƙata a madadin alhazan Najeriya,” in ji IHR.