Gwamnan Gombe Ya Bai Wa Hukuma Rancen N5bn Don Samun Kujerun Hajji 950 – ES

0
82

 

Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya na Jihar Gombe ya amince da sakin Naira biliyan 5 a matsayin rance ga Hukumar Alhazai ta Jihar Gombe domin tabbatar da samun kujeru 950 na aikin Hajji kafin wa’adin kalmmala biyan kuɗi da Hukumar Hajji ta Ƙasa (NAHCON) ta ayya, wato 5 ga Disamba, 2025.

 

Sakataren Zartarwa na Hukumar ya bayyana cewa wannan mataki ya zama dole domin kauce wa rasa guraben Hajji na shekarar 2026 ga mahajjatan jihar Gombe.

 

Ya bayyana amincewar gwamnan da yin abin da ya dace a kan lokaci domin kare muradun maniyyata a faɗin jihar.

 

Ya ƙara da cewa, sauran kujerun Hajji za a rabar da su ne bisa tsarin wanda ya fara zuwa shi ne zai fara samu, tare da kira ga maniyyata da su gaggauta kammala biyan kuɗinsu domin kada su rasa damar tafiya.