Gwamnatin Najeriya ta sanar da kamfanin sufurin jiragen sama da za su yi jigilar alhazai a Hajjin bana

0
183
Gwamnatin Najeriya ta sanar da kamfanin sufurin jiragen sama da za su yi jigilar alhazai a Hajjin bana

Gwamnatin Najeriya ta sanar da kamfanin sufurin jiragen sama da za su yi jigilar alhazai a Hajjin bana

Gwamnatin Najeriya ta amince da kamfanonin jiragen sama hudu da za su yi jigilar alhazai zuwa aikin Hajjin bana a kasar Saudiyya.

Shugaban Hukumar Alhazai ta Ƙasa, NAHCON, Farfesa Abdullahi Usman, ne ya sanar da hakan ta wata sanarwa da Daraktar yada labarai ta hukumar, Hajiya Fatima Usara, ta fitar a jiya Lahadi a Abuja.

A cewar sanarwar, kamfanonin jiragen da aka amince da su sun hada da Air Peace Ltd., Fly-Nas (kamfanin jirgin saman Saudiyya), Max Air, da UMZA Aviation Services Ltd.

Ta ce an zaɓi kanfanoni huɗun ne daga cikin 11 da su ka nemi a basu kwangilar.

“Wannan tantancewa, wadda Kwamitin Tantance Jiragen Sama mai mambobi 32 ya gudanar, an fara ta ne a ranar 26 ga Nuwamba, 2024, tare da wakilai daga Hukumomin Jin Dadin Alhazai na Jihohi da hukumomin sufurin jiragen sama, irin su Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Sama ta Ƙasa (NCAA), Hukumar Filayen Jiragen Sama ta Tarayya (FAAN), Hukumar Gudanar da Sararin Samaniyar Najeriya (NAMA), Hukumar Kula da Yanayin Sararin Samaniya (NIMET), da Hukumar Binciken Hadurran Jiragen Sama ta Najeriya (NSIB).

“Shugaban NAHCON ya kuma ja hankalin kamfanonin wajen samar da ingantaccen aiki a yayin jigilar alhazan,” in ji Sanarwar.