Sama da maniyyata 1,000 sun biya dukka kuɗin aikin Hajjin bana a Jigawa

0
131

 

Hukumar jin dadin alhazai ta jihar Jigawa ta ce sama da maniyyata 1,000 daga jihar sun biya cikakken kudin aikin Hajji na N8, 457, 685 na aikin hajjin bana.

 

Babban Daraktan Hukumar, Alhaji Ahamed Umar Labbo ne ya bayyana haka ga manema labarai a Dutse a yau Alhamis.

 

Ya bayyana cewa sama da kujeru 1,000 da aka siyar na daga cikin 1,809 da hukumar alhazai ta kasa NAHCON ta ware wa jihar.

 

Ya kuma ce a yanzu haka kusan duk shirye-shirye na aikin Hajjin bana sun kammala, inda ya hori jami’an hajji na jihar da su yi aiki tukuru tsakani da Allah domin samun nasarar aikin Hajjin 2025.