Hajjin bana: Rukunin malamai na NAHCON sun yi wa Tinubu da Nijeriya addu’a a Madina

0
134

Hajjin bana: Rukunin malamai na NAHCON sun yi wa Tinubu da Nijeriya addu’a a Madina

Rukunin malamai da Hukumar alhazai ta kasa NAHCON, ta dauki nauyin zuwan su Saudiyya domin wayar da kan alhazai a Hajjin bana, ya shirya addu’a ta musamman ga shugaban kasa Bola Tinubu da shugabannin Najeriya akan Allah ya taimakesu ya kawo karshen rashin tsaro da kawo sauyi a kasar.

Shugaban Majalisar Limamai da AIfas na Etiosa a Jihar Legas, Sheikh Afini Yusuf AbduIbari ne ya bayyana haka yayin da ya ke zantawa da manema labarai a Madina a jiya Juma’a.

AbduIbari ya ce makasudin yin addu’ar shi ne addu’a ga al’ummar kasa da shugabanninta, musamman shugaban kasa kan ayyukan alheri da ya ke yi.

“Shugaban kasa na aiki tukuru tun lokacin da ya shiga ofis, kuma bai nuna gajiyawa ba a yau, don haka muna bukatar mu ci gaba da yi masa addu’a, dalilin da ya sa muka zo nan.

“Mu na kuma addu’ar Allah Madaukakin Sarki da Ya taimake mu a kan rashin tsaro a cikin al’umma, muna addu’a ga daukacin tawagarsa da dukkan jami’an siyasa,” inji shi.