Allah Ya yi wa Hajiya Jamila Muhammad rasuwa a ranar Litinin, 2 ga watan Yuni, 2025 a Saudiyya.
Marigayiya Jamila na ɗaya daga cikin mahajjatan bana daga Jihar Filato, inda Allah Ya yi mata cikawa a Asibitin Sarki Abdul’aziz da ke birnin Makka biyo bayan taƙaitaccen rashin lafiya.
Sakataren Hukumar Alhazan Jihar Filato, Daiyabu Dauda, ya tabbatar da rasuwar. Inda ya ce da farko ya ba da umarnin a ɗauke ta zuwa asibiti domin samun kulawar likitoci daidai da umarnin Gwamna Caleb Manasseh Mutfwang.
Ya ƙara da cewa Amirul Hajj na jihar tare da wasu jami’ai da ‘yan uwan marigayiyar na daga cikin waɗanda suka halarci jana’izar marigayiyar wadda aka gabatar daidai da karantarwar addinin Islama.





