Gwamnan Sakkwato ya baiwa kowanne mahajjaci Naira dubu 450 a Makkah

0
138

 

Kowane mahajjaci, daga cikin mahajjata 3,200 daga jihar Sakkwato ya samu Riyal 1000 na Saudiyya wanda ya kai Naira dubu 450,000 a matsayin barka da Sallah daga Gwamna Ahmed Aliyu na jihar.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a ranar Asabar,  yayin wata ziyara da ya kai sansanin alhazan Sakkwato a Minna, inda ya taya su murnar kammala aikin Hajjin bana.

Aliyu ya ce an yi hakan ne da nufin tallafa wa alhazai da kudade a lokacin da suke shirin dawowa gida Najeriya.

Ya bayyana jin dadinsa da yadda mahajjatan jihar ke gudanar da ayyukan hajjin bana, inda ya ce babu wanda aka samu ya saba wa dokokin Saudiyya a lokacin zamansu a kasa mai tsarki.

“Ina so in gode muku sosai saboda kasancewa jakadu na kwarai na jiharmu a wannan kasa mai tsarki, hakika ina alfahari da ku,” in ji gwamnan.