A kokarin ta na ci gaba da zaburar da ma’aikatan ta, Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Jigawa ta ce za ta shirya taron bitar sanin makamar aiki ga jami’an ta dake dawainiya da alhazai a gida da kuma kasa mai tsarki.
Darakta Janar na hukumar, Alhaji Ahmed umar labbo ya bayyana haka bayan kamala taro na musamman da shugabannin sassa na hukumar da aka gudanar a shelkwatar hukumar dake Dutse babban birnin jihar.
Yayi bayanin cewar, hukumar zata bada bitar ne ga jami’an da kuma shugabannin shiyya-shiyya kan hanyoyin kara kula da walwala da jin dadin maniyyata da kuma dabarun magance kalubale yayin gabatar da aikin hajji.
Yana mai cewar bada horo na da matukar mahimmaci duba da yadda aka fara biyan kudin kujerun aikin hajjin 2026.
Alhaji Ahmed Umar Labbo, yace tuni shirye-shirye sunyi nisa waje fara shirin dunkarar aikin hajjin shekarar 2026.
A cewar sa, tsarin gudanar da aikin hajjin wannan shekarar yasha bam-bam da na shekarar 2024.
Yayi nuni da cewar, a bana, 8 ga watan Oktoba wannan shekerar da muke ciki itace ranar karshe ta biyan kudin kujeran aikin hajji kamar yadda hukumar kasar Saudi Arabia ta bayyana.
A sabili da haka nema Labbo yayi kira ga maniyyata aikin hajjin badi da su gaggauta biyan kudin ajiyar su na naira miliyan 8 da dubu dari 5 kamar yadda hukumar aikin hajji ta kasa NAHCON ta bayyana.
Ahmed Labbo, ya yabawa Gwamna Umar Namadi bisa kula da ayyukan hukumar a kowane lokaci.
NAHCON dai ta baiwa Jihar Jigawa kason kujeru fiye da 1,600 na maniyyatan aikin hajjin.
Source” frcn





