Hukumar Alhazai ta Jihar Bauchi ta gudanar da ziyarar wayar da kai a Karamar Hukumar Toro domin sanar da al’umma muhimmancin biyan kudaden aikin Hajji na shekarar 2026 da wuri, tare da warware tambayoyin da suka shafi shirin hajjin bana.
Babban Sakataren Hukumar, Dr. Abdurrahman Ibrahim Idris, ya jagoranci tawagar hukumar, inda suka samu rakiyar wakilan AL-UMMA da kuma wasu masu fada aji daga cikin al’umma domin tabbatar da isar da wannan saƙo ga maniyyata.
Shugaban Karamar Hukumar Toro, Pharmacist Ibrahim Tanko, ne ya tarbi tawagar a madadin al’ummar karamar hukumar. Yayin taron, ya godewa hukumar bisa wannan ziyara tare da tabbatar da cewa hukumomin karamar hukumar za su ci gaba da hadin kai wajen wayar da kan jama’a domin ganin shirin hajjin na shekarar 2026 ya samu nasara.
A jawabinsa, Dr. Abdurrahman ya jaddada cewa wajibi ne maniyyata su yi gaggawar biyan kudaden hajji domin gujewa cunkoson lokaci da matsalolin da ke faruwa idan aka yi jinkiri. Ya kuma bukaci masu niyyar zuwa hajji da su yi amfani da wannan dama wajen shirya kansu tun da wuri.
Taron ya gudana cikin nasara, tare da halartar wakilai daga bangarori daban-daban na al’umma, inda aka sake jaddada bukatar hadin kai domin ganin dukkan maniyyatan Bauchi sun samu damar gudanar da ibadar Hajji cikin sauki da kwanciyar hankali.





