Hajjin 2026: Zarge-zargen ƙumbiya-ƙumbiya sun biyo bayan zaɓen tawagar ma’aikatan wucin gadi na kiwon lafiya da NAHCON ta yi

0
275

 

Hajj Reporters Hausa

 

 

An fara bayyana damuwa game da tsarin zaɓen tawagar ma’aikatan kiwon lafiya na Hajjin 2026 da Hukumar Hajji ta Ƙasa (NAHCON) ta yi, biyo bayan zarge-zargen cewa an zaɓi kusan ma’aikata 200 a ɓoye ba tare da bin ƙa’idojin da aka tanada ba.

 

Wata majiya da ke da masaniya kan lamarin ta yi zargin cewa an kammala zaɓen tawagar likitocin ne kwana guda kacal bayan NAHCON ta buɗe gayyatar neman aiki ga jama’a, tare da ikirarin cewa shugaban hukumar ne da kansa ya jagoranci aikin zaɓen.

 

A cewar majiyar, zuwa yanzu ana kammala aikin kin bizar mutanen da aka zaɓa, alhali kuwa a yadda abin ya nuna ya kamata ace yanzu haka ana an kammala tantance waɗanda aka zaɓa ne.

 

Majiyar ta kuma yi zargin cewa an buɗe shafin yanar gizon neman aikin ne kawai ga waɗanda aka riga aka zaɓa tun farko, sannan aka rufe shi nan take bayan sun kammala cike fom ɗin, lamarin da ya hana sauran masu sha’awa samun damar nema. Haka kuma, an ce ba a gudanar da tattaunawar tantance masu neman aiki ba, wato (interview), sabanin abin da aka saba yi a baya wajen zaɓen tawagar likitocin aikin Hajji.

 

Wasu masu nema sun yi korafi ta shafukan sada zumunta na Independent Hajj Reporters, inda suka bayyana cewa ba a taɓa tuntubarsu ko aiko musu da saƙon tabbatar da karɓar takardun su ba, kamar yadda aka saba yi a shekarun baya.

 

Wata mai suna Aisha Ahmad, wadda ta nemi aikin jinya (Nurse), ta ce tun bayan da ta cike fom ɗin a yanar gizo ba ta samu wani sako ko amsa ba. Ta ƙara da cewa abin mamaki, wata ƙawarta ta shaida mata cewa an riga an zaɓi wata da ta sani har ma ta miƙa fasfo ɗinta.

 

Da take mayar da martani kan zarge-zargen, Fatima Sanda Usara babbar darektar yaɗa labarai na hukumar ta bayyana cewa “waɗanda ke cikin jerin tawagar ma’aikatan kiwon lafiya na ƙasa a halin yanzu su ne waɗanda aka riga aka zaɓa kuma aka tantance su a bara, amma ba su samu damar tafiya ba saboda matsalolin samun biza.

 

Haka kuma, an tantance waɗanda jihohi suka gabatar a ranar Talata, 3 ga Fabrairu.” Ta ƙara da cewa sauran waɗanda aka gabatar da sunayensu za a gayyace su domin tantancewa, amma ana jiran amsa daga ɓangaren Saudiyya kafin a yanke shawarar mataki na gaba.

 

Ta jaddada cewa “NAHCON za ta ci gaba da gudanar da dukkan naɗe-naɗe da zaɓe bisa ƙa’idojin da hukumar ta tanada.”